NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA A sanyaye Jummai ta kada kai, Oh na fahimata”, Aljanin Tanimu yace, “Yauwa! Ai shi wannan auren sai mutum ya Kasaita yake yin sa, kamar dai ke din nan”Jummai ta sake kada kai, murna da dan tsoro na zagaya kanta. Dakin ya jima shiru, sai can cikin kakkausar murya Aljani Tanimu yace mata, “Zaki auri shi wancan Gwamnan Aljani, nan da sati biyu zai zo ku gana, zai ‘taho miki da kudin « aure milyan hamsin, na bar ki lafiya”. Sai Jummai taji Kit! An datse hayaniyar da ta cika dakin hade da muryar tasa, Kamshin da ya cika dakin kuma ya fara raguwa. Boka Salmanu ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya yana dubanta, Gaskiya ke mutum ce mai sa’a”. Jummai ta kantamo murmushin murna dana yaKe ta gwamutsa, muryarta na rawa tace, “Boka ta yaya wannan lamari zai yiwu?” Salmanu ya kawar da kai yace, “Ai ba dole ba ne, na sani zabi ya baki, in ba kya son kudin ai zaki iya fasa auren”. ZAMU TASHI Ta zabura,Yay…