NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 13 KARSHE END BY MAIMUNA IDRIS SANI
BELI
NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 13 KARSHE END BY MAIMUNA IDRIS SANI
BELI NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 13 KARSHE END BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Salmanu ya kawar da kai wani shegen haushi na naushinsa a Kirji. Ai a duniyar nan duk wanda yayi maka sihiri ya juyar maka da lissafi ya gama da kai, wai sammatacce irin Adamu ne ke fatan matarda ta sammace shi. bata zuwa wajen bokaye, wannan kayan takaici da me yayi kama? Ga abin duka Adamu, amma babu dama. Tanimu dayake shi ma wani gabon ne kawai sai ya karkace kai yace, “Yo Adamu wannan kundubar matar taka in ba ta je wajen boka ba, ta ya za’a yi ka zauna da aurenta? Ni wallahi ko da marsandi aka hada min ba zan zauna da wannan raka ni kashin ba, aiba ta da wani amfani in ba kashin tsakar dare ne ya rarako mutum yana tsoro kuma ya rasa dan rakiya…” Da dai Salmanu ya lura da cewa duk hararar da yake wa Tanimu bai kula ba kuma ba shi da niyyar diga aya nan kusa a kundin cin fuskar da ya budewa Adamu, kawai sai ya dauki wani kofin ruwa ya jefe shi da shi, ciki…