NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Suna fita Salmanu ya tashi ya fada ciki ya lalubo Adamu a duhu. *Adamu ina mukullin dakin nan da muka ce zamu fara karbar mahaukata mu tara su a nan?” Www.bankinhausanovels.com.ng Cikin damuwa Adamu ya ce, Salmanu su zaka mayar mahaukatan?”Salmanu ya bata rai, . – “Haka na fada maka?”. Adamu ya cigaba da kallonsa kawai cikin duhu Hakan ya sa Salmanu Kara bayani, Zan ajiye su zuwa yamma, akwai shirin da nake musu, ni babu dan iskan da zai taba ni sannan ya shigo hannuna in bar shi ya wanye lafiya’Adamu bai damu da manufar maganar Salmanu ba sai zagin da yayi. Cikin nuna jimami ya ce, “Salmanu ka tuba, ka ce zagin da ka yi ban da MAhaifinka a ciki”Kai tsaye Salmanu ya amsa, . “Ni dama ba shi na zaga ba”Adamu ya san dai fada kawai Salmanu yayi, amma babu yadda ya iya haka ya yarda da shi, kuma ya je ya nemo masa mukullin, suka. fice tare ta Kofar baya ya kai wa Tanimu, …