ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 4  CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir                 Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana gaza samarwa kaina wadannan amsoshin guda biyu, sai kawai na fita, ina juyowa muka hada ido yana kokarin fitowa daga nashi dakin janye da (travelling bag) mai matsakaicin girma ‘troller’ ruwan zuma. Dammm! Naji kirjina ya buga, bugawar da ba’a kirjin kadai ta tsaya ba ta hudo ne har cikin zuciyata. Sanye yake da riga fara anyi rubutu da shudin zare ‘TOMMY HILFIGER’ da shudin wandon (jeans) turrare, sumar nan ta kwanta tayi luf a saman kansa sai sheki take, inda duk ya motsa sassanyan kamshin ‘212’ ke tashi.. Ya saya kwayar idanunshi cikin gilashi ‘porsche’ mai duhu ainun, don haka kai tsaye ba zan iya cewa ga halin da kwayar idanunshi ke ciki ba. Ya ajiye jakar a kusa dashi ya zauna a kujera sosai ya zage zip dinta, ya ciro katin ATM ya dago ido ya dubeni ina tsaye a inda nake ban ko motsa ba. “Ko zaki iya zama?” Abinda ya ce dani kenan. Tamkar wata rakuma da akala na bi umarnin furucin…