YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Wani irin farin ciki da murna suka lullube jarumi Idrisu, ganin cewa dokinsa da ya dade babu lafiya ga shi yau ya ji sauki kuma ma kamar ya fi shi zakuwar haduwa da abokan gaba, ai nan take Idrisu ya dauke sirdin dokin da ke kan dardumar da ya ke ta yaki a kanta ya dora wa doki abinsa, ya nade dardumar tashin ya saKala a kurciyar sirdi. Doki yana jin an hau “shi sai ya yi wani irin rimi ya dire, ya daga kafafuwan baya ya harbi iska sannan ya zabura ya nufi inda su Bakayalu suke. Aka hade a tsakiya, su biyu kadai, jarumi Idrisu dan > Hamidu da tsohuwar aljana Bakayalu. ALJANA Bakayalu ta ce masa, “Kai dan Adam! Me kake bukata ne haka kake ta kashe mana jama’a babu dalili?” Jarumi Idrisu ya amsa mata cewa, “Ranki kawai nake son dauka, ke da azzalumin jikanki Sham’‘una saboda irin mugun zalunci da kuka dade kuna yi.” Cikin fushi sai ta ce masa, “Kai Karamin alhaki! Ka sa…