YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Shi dai bai ga mai magana ba, alhali kuwa ga dadin maganar ya daki dodon kunnensa, sannan kuma ga Kanshin turare yana ta zagaye hancinsa yana kaiwa zuwa ga zuciya da kwakwalwarsa, sai ya ce, “Ya mai wannan magana mai dadi, na dai san cewa mace ce, Www.bankinhausanovels.com.ng kuma na san na taba jin muryar, saboda haka in dai babu yaudara, to ya kamata a fito fili. In kuma an Ki, to babu ko shakka ni zan ci gaba da tafiyata don na zaku da ganin abin da ya fito da ni.” Shiru kake ji. Idrisu ya mike zai tafi, sai ya ga an dan daga labule, sai ga wata yarinya wadda duk wanda ya ce zai siffanta hakikanin kyanta, to babu ko shakka zai zalunce ta ta hanyar rage ambaton wani abin. Suna hada ido sai gaban Idrisu ya fadi, kuma babu abin da ya fado masa a cikin zuciya sai kamannin yarinya Nur da ya taba hangowa daga nesa. Yana Kokarin tantancewa shin ashe a duniyar nan akwai kyakkya…