YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 17 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 17 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 17 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Nan fa suka shiga Karaji wai su manyan jarumai, Www.bankinhausanovels.com.ng amma sai dai kash, akwai wani babban abin da ke damun su, wato rashin Karfin jiki a dalilin dafin da Sarauniya ta taba shayar da su. Ita ta san cewa a irin wannan halin da suke ciki sai dai kururuwar kawai, don ko bera ba za su iya kamawa ba, saboda haka sai ta dauko wata katuwar gora ta fuskanci jaruman nan, kuma tana sane ta yi kamar ba ta sani ba ta kyale lullubin fuskarta ya yaye, ta yadda dumbin kyan da ke dankare a fuskarta ya bayyana har jaruman suka gani sau daya sannan ta yi sauri ta rufe. Ai fa wannan sai ya Kara tunzura tare da haukata su wurin hankoron fita don cinye wancan jarumi. Babu ko tantama sun isa jarumai, ballantana kuma ga shi sun huta, an kiwata su sun yi bulbul. Kafin wani lokaci ta sa duk an dora wa dawaki sirada, kuma kafin kowane jarumi ya hau sai ya amshi moda daya…