RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA  BOOK 2   CHAPTER  8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO                  Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA Nan da nan annurin fuskar wacce aka kira da shugaba ya bace bat! “Ke! Kada ki kawo mana zancen banza kin ji? Ya zama dole ki kawo mahaifiyarki da kanki ba sako zan ba wani ya kawo min ita ba, albarkar da ) na samu agun iyayena kafin su bar duniya, sai kowannenku ya sami wannan albarkar. Za ki kawo ta ko kuma sai na dauki mataki akanki? Zan iya daureki shekaru dari ina gana maki azaba, bayan kuma na daukota da Karfin tsiya.” Sake KasKantar da kanta tayi, “Ina neman tuba ya shugabata. Na amince zan kawo mahaifiyata da ranta. Farin cikinki a kullum shi ne nawa.” A nan suka yi wasu maganganu wanda su kadai suka san abinda suke cewa. Sannan aka ba wani wuka ya karba yana mai sake rusunawa alamun girmamawa. Wannan yarinyar da ke kwance kawai ya caka mata wukan, wanda yasa Nawfal gigicewa ya ture wani abunda bai san ko mene ne ba, jikinsa babu inda baya rawa. A gigice suka walwayo…