RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Sultan ya gyada kai yana dubanta, “Za mu mayar da ku gidanku, zamu sa ‘yan sanda su kula da shige da ficenku. Ina buKatar sanin inda zan je inga Sani a kwana biyu kacal. Kada’ki wuce hakan. Maganar miliyan dayanku da muka yi maku alkawan ‘yan sandanmu za su tafi maku da kudin sai kuyi amfani da su. Ya zama dole mu gano wanene azzalumin da ya aikatawa Saudat fyade ya kuma aika aka kasheta.” Sai da aka fice da su kafin suka zubawa juna ido da alama sun rasa mafita. Ashmaan ya fara magana yana duban su, “Zan watsa hotunan Saudat a duniya, zan rubuta muna neman wanda ya kasheta, akwai kyauta mai tsoka. Bayan nan da wasu kwanaki zan watsa hotunan Nasreen da Nawfal in kuma ambatar babban kyauta ga duk wanda Allah yasa ya gansu.” Mahbub ya dube shi a tsanake, “Mene ne fa’idar yin hakan?” Aslaf ya zare glas din idanunsa yana sake duban Ashmaan, “Idan kayi hakan ZAMU TASHI Ashmaan za a sami matsal…