RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA  BOOK 1  CHAPTER 7  BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng  A JIYA MUN TSAYA  duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.” Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.” Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.” . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu ” sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar m…