ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 2

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 2
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 2 Khadija (Ummi) ita kadai ta fara cin sunan Hajja a cikin mu. Diya ce ga Aunty Hauwa dake Kaduna. Ummi tun tana shekara biyar Aunty Hauwa ke kawo ta hutu wajen Hajja su hadu ita da Zanirah suyl ta wasa, Zuwan ta ya zama akai-akai duk hutun makarantar boko. Da dai Ummie ta gane irin dabdalar da yara sa’o’inta ke yi a gidan Hajja sai ta yiwa uwarta tawaye ta shiga ihu da tirjiya duk lokacin da aka zo tafiya da ita gidansu.  In kuma aka takura mata tafiyar, to a ranar duk gidansu ba mai barci da shesshekar kakanta har da shidewa. Dole iyayenta suka hakura da kulafucinta suka bar ma Hayja.  Ni FA’IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA, ina daya daga cikin jikokin A.B Family, kamar yadda na fada a baya, mahaifina shine da na biyu a ‘ya’yan Hajjah wato Professor Ahmadu Bamalli na jami’ar Ahmadu Bello. Auren zumuncin Bamalli shi ke tsakaninshi da Mamana Maimunatu da muke kira Momin ABU, shi kuma Baban ABU.Nice ta fari, sal  Abdallah, Walida ke bin Abdallah. Yayin da Kausar ta kasance …