ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 1
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 1 Da ka doso garin Giwa gidan za ka fara hanga daga gabas masu kudu na garin, tangamemen gida da aka yiwa jan rufi na zamani mai zagaye da girgijejen gate na bakin karfe da aka fi kira da Mahdi-ka-ture. Dauke yake da (estate) guda wanda ya hadiye gidaje na zamani (flat) guda goma sha biyar. Idan ka daga kanka sama, rubutu ne da aka yi da ruwan gwal mai sheki an rubuta ABUBAKAR BAMALLI GIWA ESTATE. Gidaje ne reras (dispersed) masu sanyin gani a ido da _ fenti ruwan gwaiduwar kwai. Gida daya ne ya bambanta da wadannan gidaje guda goma sha hudu wato gida na farko. Gida na farko ya fi duka gidajen girma, kuma shi kadai ne mai hawan_ bene. Mamallakiyar wannan babban __ gida tsohuwa ce ‘yar kimanin shekaru saba’in da biyar mai amsa sunan HAJIYA HADIZA GIWA, wadda ‘ya’ya_ da jikokinta ke kira da HAJJAH. Za ka yi mamaki idan ka ji cewa, duk girman gidan nan ita kadai ta yi rayuwa a cikinsa a matsayin matar gida, haka duka ‘ya’yayen nan goma sha biyar ita ta haife abinta …