RAYUWAR ASMAU CHAPTER 8

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 8
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 8 Satin Yaa Aslam daya ya juya da shirye shiryen bikin su. Dan yana komawa yasa Momy a gaba dole suje dubai su hadu kayan lefe. Momy ta ce, ya bari lokaci ya kara karatowa. ‘Ki yayi ya ce shidai su tafi. A satin da ya dawo a satin suka tafi hado lefe. Siyayya mai yawa da tsada sukayo. Duk abinda yaga ya burge shi ya ce a dauka. Haka nan Momy itama da ta iya zabe kaya masu kyau da tsada ta dinga siya. Kaya sai da suka hada set akwati uku amma basu isa ba. Sosai Momy ta hado mata kayan kwalliya da english wears dan ta san irin shigar da Asma’u take kuma tasan Asma’u yar gayu ce. Haka suka dawo gida da niki nikin kaya. Shi Dady da ya gani ma cewa yayi sunyi kadan. Kudi ya bayar a dado kayan da gwala gwalai. Har da Mota Dady ya ce a hada mata. Momy tace, “Dady ai ba yanzu za akai kayan ba.” Dady ya ce, “Me za’a jira to. Kunga akai kaya ai sa rana kawai komai yazo daga baya.” Momy ta ce, “To Dady in haka ne, ai kune masu kai kayan dan na fison maza suyi komai. Mu masha biki daga ba…