ZUCIYA CHAPTER 23

ZUCIYA CHAPTER 23
ZUCIYA CHAPTER 23 Ya dade a waje kafin zuciyarsa ta daidaita ya dawo gida, har ya kusa isa gida ya kira Anisa, ta d’aga cikin tsananin farin ciki, yace ” Nisa kina ina?” Tace ” ina nan gidan su Zee.” Yace ” bari nazo na daukeki.” Wani dadine ya kamata suna kashe waya ta saki wani ihu na farin ciki gaskiya yanzu ta aminta da san da Ashraf yake mata, nan Zee taita tsokananta wai ta dinga ja mai class, itakam ita kadai tasan abinda ta gani da yanda taji asanda ya juya mata baya.+ Ashraf yai shiru bayan sun gama waya har yanzu yana mamakin kawu, ya sani sarai mutum ne mai tsananin ambition sai dai bai taba tunanin haka b’oyayyun halayensa suke ba, da har zaiyi threatening din mahaifiyarsa da yakeso akan laifin da yayanta dashi suka aikata akan ta aureshi, shiru yai yana tunani kafin yai gwafa sannan ya kira Dan Litti, bugu biyu ya daga. Ashraf yace ” Dan Litti ka nutsu sosai ka ji mai zanje maka.” Nan ya shiga mai bayani da ni kaina bansan me suke cewa ba sai dai sunkai kus…