ZUCIYA CHAPTER 22
ZUCIYA CHAPTER 22 Bayan sun zauna Malam ya kalli Ashraf wanda ya nutsu yana kallansa.+ Ashraf ganin Malam na kallansa baice komai ba yace ” Malam ya akai?” Malam yai murmushi yace ” tunowa nai lokacin da mukai wannan tafiyae bakafi dan haka ba ” ya fada yana gwada tsayin Ashraf a lokacin. Ashraf yai kasa dakai yana murmushi. Malam yace ” A wannan rana munje kauyuka da dama na kusa da na nesa, a karshe muka isa wani gungurmin kauye, wanda ‘yan garin kana ganinsu kasan suna cikin tsananin wuya da talauci, nan muka isa gun mai garin aka tara ‘yan garin aka fara basu sadaka, kaima kana mikawa. Gun yayi cunkoso wanda ya janyo turereniya agun, wasu suka dinga faduwa saboda karfin da kowa yake gwadawa. Ganinka mukai kabar gun rabon da dan gudunka. Nan Abbas ya leka ya ganka gaban wani bawan Allah, tsoho ne tukuf gaba d’aya gashin kansa fari ne ya tsufa sosai, wanda aka tureshi garin rigima ya fadi kasa. Da saurinka ka karasa kana neman d’aga mutumin, tsohon wanda kowa yake kya…