SOYAYYAR MU CHAPTER 5

SOYAYYAR MU CHAPTER 5
SOYAYYAR MU CHAPTER 5 Akwai wata rana a gidan Ammi, Aisha da Hanifa zaune a qasa a qaramin falo suna rubuta list din kayan da suke buqata na hada kek yayinda Nafisa take bisa kujera tana kallon TV. Wayar Aisha ce tayi ringing, a wannan lokacin kuwa wayar tana kusa da kujerar da Nafisa take zaune don haka ne ta yunqura ta janyo wayar don miqa ma Aisha wadda bata ma ji wayar tana ringing ba. Sunan Yusuf ta gani a fuskar wayar A wannan lokacin ne Aisha ta ji qarar wayar ta nufo wurin Nafisa ta karba. Ko da ta amsa wayar bayan sun gaisa ne yake ce mata zai zo anjima wanda ta amsa mishi sannan ta kashe wayar. Nafisa ce tace “waye wannan Yusuf din?” Aisha tace “Anty saurayi na ne wanda zan aura ” shine ake wani yi mishi yanga kamar ba”a so?” Aisha a ranta tace bana ma son shi, qanin ki nake mutuwar so, kawai banda yadda zan yi ne. Hanifa ce tace “haba Aisha ashe kin kusa aure shine ko da wasa baki taba gaya mana ba?” tace nima ai ban dade da sani ba tunda Baba na ya samu da maganar ba ni ba, kuyi ha…