MRS AMIDUD CHAPTER 3

MRS AMIDUD CHAPTER 3
MRS AMIDUD CHAPTER 3 Washe hakori tayi sannan tace. “Baffana! Ince idan nayi auren anan zan zauna!?” “Ai dole ma ki zauna a nan!” Alhaji Muhmood yace mata. “Toh Baffana waye min!” Tasaka hannu a habb’arta! “Eh toh! Nima ban san shi ba, sai Allah ya kawo miki.” Shiru tayi dan tunanin ta duk ya kulle, can tace. “Toh ita wancar doguwar waye Zata aura?” Shiru yayi yana kallon Mamie, girgiza kai tayi sannan tace mata. “Ai ita matar Yayan kuce!” Tura baki tayi kamar zatayi kuka tace. “Toh wallahi a nimo min mijina ko kuma na hanasu auren” Zaro ido waje suka yi, tare da jinjina kaurin kan Parih dakyar suka lallaba ta, ya bar falon.+ Bayan tafiyar Lamisah tayita mita, ita bata ga wani abin burgi a jikin Lamisah ba. “Haba ku baku ga yadda take ba mutum sai kace sanda rake” Babu wanda ya kulata haka ta gama mitarta har tayi barci a gurin. Bayan sati uku sai gasu Fahhamah da Fahmeedah, sun zo huta dake suna karatunsu n…