TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 11
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 12 Buɗe baki yayi don ya mayar mata da martani, Amma ya kasa cewa komai dan takaici, kallon ta ya ke in da har lokacin ta dage tsakanin ta da Allah neman maganin ta take. A fusace ta sake waigo shi ta ce “Wai dan Allah Saif menene haka?” Can ta sake wani tunani, cikin sigar kissa da tausasa murya ta ce “Saif wani kwallin magani na ke nima, dan Allah ba ka gan shi ba?” Hankali kwance ya na mai ɓoye ɓacin ransa ya amsa da “Wani cikin ɗan karamin kwali haka? An rubuta post pill kamar?” Ras gaban ta ya faɗi, ta na mai fatan Allah ya sa bai karanta kwalin maganin ba ya san maganin menene ta ce “Exactly, shi ne, maganin ciwon mara na ne” Sai da ya tashi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce “Eyaaaa Ina ga wani daban na gani ba wanda ki ke magana ba” Ta na mai hadiyar yawo dan jika makoshin ta tsabagen tashin hankali ta ce “Ba ni wanda ka gani din…..” “Ni na ce mi ki na ga wani abu?” Idanun ta na mai kawo ruwa ta ce “Saifullahi don’t play sm…