RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 2
RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 2 Arude su Abdul sukayi kansa suna salati, shi kansa dad hankalinsa yayi mutukar tashi amma hakan baya jin zai sakashi ya kyale sawwam ya zauna da ummulkhairi a matsayin matarsa,+ “Kagama suman ka katashi ka sakar min yata ayanzun nan zan sake daura mata wani sabon auren wanda yafi dacewa da ita…” Baban ummulkhairi yafada cikin daurewar fuska, yayun ummulkhairi ne suka matsa kusa dashi suna tambayar abinda yafaru sannan suna bashi hakuri, Wata uwar tsawa ya daka musu wacce ta razanasu, “Babu ruwanku ackin wannan lamarin, shi yasan waneni ni, sannan yasan dalilina nayin haka, kuma kamar yadda nafada ko da dansa zai mutu to tabbas sai ya sakar min yata domin shima ina son ya dandana bakin ciki kamar yadda na dandana a baya…” “Zai sakar maka yarka kamar yadda ka umarta domin ba ita kadaice macen da ta rage ba, yanda ka isa da yarka to nima zan nuna maka cewar na isa da dana….” Dad din sawwam ya fadi tareda wucewa fuuuuuuh ya nufi inda su Abdul ke kokar…