WATA BAKWAI CHAPTER 2

WATA BAKWAI CHAPTER 2
WATA BAKWAI CHAPTER 2 Ya sha bacci sosai dan jiya da dare sam bai samu wani baccin kirki ba. + Babban falo ya fita hankalin shi a kwance. Bai zaci ganinta a falon ba. Zuciyarshi ta wani doka a yan mintina kadan ya manta da damuwarsa idanuwansa suka natsu wajen aika masa da saqonni kyawun yarinyar da take zaune a falonsa. Hankalinta gaba daya yana kan kallan da take da alama ma bata san shigowarsa ba. Wannan ce natacciyar da aka aura masa kenan to kyawunta bazaisa yaji komai ba yake fadawa kansa. Dan ya tsani makwadaita masu son abun duniya. Kujera ya samu ya zauna can nesa da ita. sai lokacin ta dago ta kalle shi ta sake maida hankalinta kan T.V din kaman baya wajen. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Sam bai saba mace ta kalle shi tai kaman baya nan ba duk min ajinta kuwa. Yana da kyau shima yasan hakan. Duk macen data kalle shi saita qara kallansa amman ta wani basar kaman bashi bane zaune a wajen. Ballantana kuma in tasan koshi waye yanzun zakaga yarinya nasan yai mat…