WANENE SHI CHAPTER 6

WANENE SHI CHAPTER 6
WANENE SHI CHAPTER 6 Ya d’ago da kansa a hankali sanda aka rufe main kofar shigowa falon. “Watarana idan na gaji, zan shak’e wuyanka ne kowa ya huta.” Imran ya juyo daga cire takalmansa da yake ya kalli jaamil dake zaune daga kujerar dining na falonsa. “Yaushe kazo? Ka dade kana jirana ne?” “Tun sanda ka bar wajen aikinka ka tafi yawon zagaye gari nake zaune anan.” Imran ya k’araso da murmushinsa. “Toh me yasa kawai baza ka dawo nan bane, kaga ka huta zirga-zirga, kuma akwai spare d’aki…biyana kawai zakayi ka shiga.” Jaamil bai saurari k’arshen zancen nasa ba ya kalli ledar daya ajiye akan table din. “Meye wannan kuma?” “Abinci ne nayi takeaway, don har yanzu bana jin k’arfin jikina, ba zan iya girki ba.” “Wai me yasa ka damu kanka da abincinsu ne?” Ya d’aga kafada kad’an. “Saboda yana min dadi.” “Ranar da komai zaizo karashe zanga yadda zakayi.” “Me kuwa zanyi, zan cigaba da zuwa ne ina siya.” Har jaamil zai bashi amsa suka tsinci knocking daga k’ofa. Ya juyo ya kalleshi. “Meye kake kallona? Gidanka …