WATA SHARI'A CHAPTER 7 WATA SHARI’A CHAPTER 7 Bayan sati daya na farajin sauk’i, harzama na farayu sabanin da da ko zaman ma bana iyawa, Sosai Dr. Rafl’iq yake bani kulawa, komai shi yakeyi min, hatta da magani da kanshi yake siyamin ya bani ruwa insha, Kawayena Zarah da Rabiatu kuwa tamkar ‘yan uwana na jini, duk wani abu daya dace suna yiminshi, Abun haushi kuwa har yanzu Gentle batazo da dubani ba. Kwatsam ina zaune Rabiatu da Zarah na gefena, labari muke sosai suna bani dariya, hakan yasa hankalina yadan kwanta, a gidanmu kuwa har yanzu basu sani ba, saboda Dr. Raflq yace kar in fada masu abunda ya sameni harsai idan na koma gida dan kar in tayar masu da hankali. Securities ne suka shigo roon din har mutum hudu, bayansu kuwa wani babban mutum ne sanye da babbar riga, Bayan shigowarshi saiga wasu securities din guda hud’u a bayanshi. Cike da girmamawa muka gaishesu, Mutumin kawai ya amsa sallamar, tun bai rufe baki ba saiga wasu manyan mutanen sun shigo masu yawan gaske, har room dinma bai iya d’aukarsu b…